Takkadama a kan janye tallafin kudin man fetur a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa a bisa aniyar gwamnati ta janye tallafin da take bayarwa ga bangaren man fetur.

Ita dai gwamnatin ta ce janye tallafin zai ba ta damar saka karin kudi ga ayyukan inganta rayuwar jama'a.

Sai dai wasu 'yan kasar na ganin hakan na nufin jama'a, musamman talakawa, za su dandana kudar su ke nan domin kila a sami hauhawar farashi da kuma karuwar kudaden dakon kaya da sufurin al'umma.

To amma yayin da wasu ke wannan hange wasu kuma gani suke duk inda ta fadi ba za ta sake zane ba.

Jam'iyyun siyasa ma na ci gaba da fadar albarkacin bakinsu dangane da batun.

Jam'iyyun dai sun bayyana matakin da cewa bai dace ba, saboda zai kara jefa al'ummar kasar ne cikin wahala.

Gwamnatin dai ta ce za ta janye tallafin ne a cikin kasafin kudinta na shekara mai zuwa saboda mafi yawan al'ummar kasar ba sa cin gajiyarsa sai wasu 'yan kasuwa kalilan.

Sai dai ta ce za ta yi amfani da kudin tallafin wajen samar da abubuwan more rayuwa.