Najeriya ta ci tarar Mikel Obi

Mikel Obi
Image caption Mai yiwuwa Mikel Obi ya taka leda a wasan na ranar Asabar

Najeriya ta ci tarar John Mikel Obi bayan da ya halarci sansanin horar da 'yan wasa a makare a wasan da kasar za ta kara da Guinea a wasan share fagen gasar cin kofin kasashen Afrika.

An ci tarar dan wasan na Chelsea dala 5,000 saboda sabawa wa'adin ranar Talata da aka dibarwa 'yan wasan na su halarci sansanin da ke Abuja.

Mikel ya zo sansanin ne ranar Laraba, sai dai jami'an ba su ji dadin abinda ya yi ba, yana mai cewa uzurin iyali ne ya hana shi zuwa a kan lokaci.

"Hukunci ne da jami'an kungiyar su ka dauka baki daya," kamar yadda mai magana da yawun Super Eagles Colin Udoh ya shaida wa BBC.

"Ranar Talata da rana aka debarwa 'yan wasan su halarci sansanin, kuma jami'ai ba su gamsu da uzurin da ya bayarba.

Guinea wacce ke jagorantar rukunin, na bukatar maki guda ne kawai domin ta kayar da Najeriya wacce a halin yanzu ta ke mataki na biyu.