Rikici ya barke a Jos ta gabas

Rahotanni daga jihar Filato na cewa an sami tashin-tashina a yankunan kananan hukumomin Riyom da Barikin Ladi da kum Jos ta gabas, inda aka samu hasarar rayuka da dukiya.

Lamarin dai ya faru ne a jiya da dare wayewar garin yau, kuma hukumomi a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin.

Lamuran dai na zuwa ne bayan da ka samu kwaryakwaryay zaman lafiya a jihar wadda ta dade tana fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa.