Sakataren tsaron Amurka ya yi gargadi kan zabtare kudade

leon panetta
Image caption Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta

Sakataren harkokin tsaron Amurka, Leon Panetta, ya yi gargadin cewar a nan gaba Amurka ba za ta samu damar cika kudin dawainiyar da kungiyar Nato ke bukata ba.

Hakan ya biyo bayanyadda kasashen turai suke rage yawan kudaden da suke kashewa a harkokin tsaro.

A lokacin da ya ke magana a Brussels gabanin wani taron ministoci na kasashen kungiyar NATO, Mr Panetta, ya ce, mutane da dama sun dauka kasafin kudin Amurka yana da yawan da zai iya cike giben da ake samu a kudaden hidimar kungiyar kawancen ta Nato.

Mr Panetta ya ce, ita ma kanta Amurka ta kanta ta ke yi, saboda zat rage dola biliyan dari hudu daga sashen harkokin tsaro a cikin shekaru goma masu zuwa.