EFCC ta kame tsaffin gwamnoni uku

EFCC ta kame tsaffin gwamnoni uku
Image caption Hukumar EFCC ta dade tana takun saka da tsaffin gwamnoni

A Najeriya Hukumar EFCC ta kame tsaffin gwamnoni uku da suka hada da na jihar Nassarawa Aliyu Akwe Doma da na Ogun Gbenga Daniel da kuma na Oyo Alao Akala.

Hukumar wacce ke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati tana yi musu tambayoyi kan wasu laifuka da take zarginsu da aikata wa.

Dukkannin gwamnonin uku dai sun bar mulki ne a watan Mayun da ya gabata.

Kakakin hukumar ta EFCC Mr Femi Babafemi ya tabbatarwa da BBC kame tsaffin gwamnonin, amma ya ce sai nan gaba ne za su yi karin haske kan abubuwan da ake zargin mutanen da su.

Har ila yau wata majiya a hukumar ta EFCC ta shaida wa BBC cewa hukumar na shirin kame wasu karin tsaffin gwamnonin.

Wasu na nuna shakku

Wasu rahotanni dai sun nuna kamen tsohon gwamnan jihar Nassarawa Aliyu Akwe Doma, ba zai rasa nasaba da wani korafi da wasu 'ya'yan jihar suka shigar a gaban hukumar ba, inda suke zarginsa da aikata wasu abubuwa da suka sabawa doka a shekaru hudun da ya shafe ya na mulkar jihar.

Suma dai tsaffin gwamnonin jihohin na Oyo Alao Akala da na Ogun Gbenga Daniel, an dade ana cece-kuce a kansu kama daga lokacin da suke mulki da kuma bayan saukarsu.

Hukumar ta EFCC dai ta dade tana takun saka da wasu tsaffin gwamnonin kasar da ma wasu 'yan siyasa, inda ta gurfanar da kusan tsaffin gwamnoni 14 a gaban kuliya.

Shahararru daga cikinsu sun hada Sanata Joshua Dariye na jihar Plato da Saminu Turaki na jihar Jigawa da Abdullahi Adamu na jihar Nassarawa da Orji Uzor Kalu na jihar Abia.

Akwai kuma James Ibori na jihar Delta wanda ke fuskantar shari'a yanzu haka a Burtaniya, da Chimaroke Nnamani na jihar Enugu da Attahiru Bafarawa na jihar Sokoto.

Sai dai wasu masu lura da al'amura na ganin yaki da cin hancin da hukumar ke cewa tana yi, bai taka-kara-ya-karya ba, ganin cewa 'yan tsirarin mutane aka iya samu da laifi - aka kuma yanke wa hukunci kawo yanzu.