Obama ya nemi Turai ta warware matsalarta

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya yi kira ga shugabannin Turai da su dauki matakai cikin gaggawa na warware matsalar basussukan da kasashensu ke fuskanta.

Mr Obama ya ce matsalar na yin barazana ga shirin farfado da tattalin arzikin Amirka.

A halin da ake ciki kuma, manyan bankuna biyu na Turai sun bada sanarwar wasu sabbin matakai na tunkarar barazanar da tattalin arzikin kasashen nahiyar ke fuskanta daga matsalar basussukan da wasu daga cikin kasashen ke fama da ita.

Babban bankin Turai ya yi tayin bada rance ba iyaka ga bankunan kasuwanci na tsawon shekara daya, sannan Babban bankin Ingila, ya ce zai cigaba da manufarsa ta zuba karin kudade a tsarin tattalin arzikin kasar.