Amurka ta kasa kawo karshen yaki a Afghanistan

Image caption Yaki a Afghanistan a yanzu ya-k- ci-yaki-cinyewa

Tsohon kwamandan sojojin kawance a Afghanistan ya ce har yanzu Amurka ba ta da masaniya kan yadda za ta kawo karshen yakin da ya kai ga mamaye kasar shekaru goma da fara shi.

Janar Stanley McChrystal ya ce Amurka da kawayenta ba su ma yi rabin zango ba a yunkurin cimma burace-buracensu, ciki har da samar da abin da ya kira halaltacciyar gwamnati a kasar ta Afghanistan.

Manufar yakin dai ita ce farauto Osama bin Laden da kuma kifar da gwamnatin Taliban wadda ta ba shi mafaka.

Sai dai jakadan Amurka na musamman a Afghanistan a wancan lokacin, James Dobbins, ya bayyana nasarorin da ya ke ganin an samu:

Ya ce; " kamata ya yi mu tuna abin da ya kai mu: a shekara ta 2001 Afghanistan ba kawai maboya ce ga 'yan ta'adda ba babbar kawa ce ga 'yan ta'adda."

Shekaru 10 da fara yaki

A yau Juma'a ne bakwai ga watan Okutoba aka yi shekaru goma da sojojin kawance, karkashin jagorancin Amurka su ka fara kai hare-hare kasar Afghanistan domin tunbuke Taliban daga kan karagar Mulki.

A wannan lokacin dai an ga mutane da dama na ta murna, bayan sojojin 'yan adawa su shiga cikin birnin Kabul.

Yara suna wasan su yadda su ka ga dama, iyaye kuma na sauraren irin wakokin da suke so.

An yi yaki ne na wasu 'yan makwanni ne kawai kafin a sauke gwamnati a wannan lokacin, amma duk da cewa an saukar da Taliban daga kan mulki an gaggara tarwatsasu.

Yawancinsu a wannan lokacin sun ketara ne zuwa kasar Pakistan, amma sai bayan wasu 'yan shekaru da su ka ga Amurka da kawayenta sun dukufa suna yaki a Iraki, sai su ka fara fara dawowa.

Mutane da dama ne su ka mutu

Sojojin Burtaniya sun fuskanci turjiya sosai a lokacin da su ka shiga yankin Hemland a shekara ta 2006.

Burtaniya kadai ta yi asarar rayuka a Afghanistan wajen mutane dari uku da tamanin da biyu, amma wajen rayuka dubu biyu da dari bakwai ne su ka salwanta daga kasashen kungiyar NATO a yakin Afghanistan.

Al'ummar Afganistan ne dai aka fi kashewa a lokacin wadannan hare-haren.

Jami'an kasashen yamma, sun amince cewa akwai wasu bangarorin Afghanistan da za'a ci gaba da zub da jini, ko bayan kungiyar NATO ta janye dakarun ta a shekara ta 2014.

Idan dai ba'a samu an sasanta da Taliban ba, mutane da dama na ganin ba za'a kawo karshen yaki a kasar ba, kamar kuma a maida hannu agogo baya ne.