Karin albashi a China zai kara ayyukan yi a Amurka

Image caption Binciken ya ce nan da shekaru goma za'a samar da aikin yi fiye da miliyan uku a Amurka

Wani sabon bincike da aka gudanar a Amurka ya ce mai yiwuwa hauhawar kudin albashi a China ya kai ga samar da ayyukan yi har miliyan uku a kasar ta Amurka nan da shekaru goma masu zuwa

Rahoton da wani kamfani mai suna Boston Consulting Group ya fitar ya nuna cewa za a samar da wadannan ayyuka ne idan kamfanonin Amurka suka rage rassansu da ke China suka koma sarrafa kayyayaki a gida.

China dai ta wuce Amurka a matsayin kasar da ta fi kowacce sarrafa kaya a duniya.

Saboda yadda kasashen Asiya ba sa biyan albashi masu tsoka ne ya sa kamfanonin Amurka da dama su ka koma sarrafa kayayyakinsu a nahiyar Asiya.

Kamfanin Boston Consulting Group ya bayayna cewa kamfononi sarrafa kayan za su farfado a Amurka nan ba da dadewa ba.

Rahoton ya ce a yayinda ake samu karin albashi da kusan kashi goma sha biyar zuwa ashirin a kowace shekara, kuma darajar kudin China na kara bunkasa idan aka kwatantashi da dala, China za ta daina zama kasar da kamfanonin Amurka za su rika amfani da ita domin sarrafa kaya cikin rahusa.

Rahoton ya yi hasashen cewa bayan shekaru goma za a iya samar da kashi goma sha biyar cikin dari na kayan da ake kaiwa Amurka daga China a cikin gida.

Rahoton ya ce za'a samar da aikin yi wajen kusan miliyan uku a Amurka a shekara ta 2020, wanda zai kuma magance rashin aikin yi da ake fama da shi a kasar da kashi biyu.

Gwamnatin Obama za ta yi amfani da rahoton a matsayin shaidar cewa kasar za ta iya yi goggayya da sauran kishiyoyinta a nahiyar asiya.