Ana ci gaba da fafatawa a garin Sirte

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An takura sojojin kanal Gaddafi a wani wuri da bai wuce kilometer muraba'i biyu ba

An ci gaba da jin karar fashewar abubuwa a garin Sirte na Libya, inda dakarun da ke biyayya ga Kanar Gaddafi ke ci gaba da turjewa kutsen dakarun majalisar rikon kwarya ta kasar.

Bayan tsawaita luguden wuta da bindigogin igwa da rokoki ne dai, dakarun majalisar rikon kwaryar suka shiga tsakiyar birnin, suka kuma takure masu biyayya ga Gaddafi a wani yanki da bai fi murabba'in kilomita biyu ko uku ba.

A ranar juma'a ma sai da sojojin majalisar rikon kwarya su ka rika kai hare-hare da rokoki da kuma takunan yaki a tsakiyar garin.

Harin ya soma tare da ruwan harsasan bindigogin atilere ba kakkautawa sannan kuma daruruwan mayaka suka dannawa zuwa tsakiyar garin.

Tuni dai fararan hula da dama suka fice daga garin.

kokarin sasantawa da mutanan dake kare garin ya faskara.

Wani kwamandan dakarun majalisar rikon kwaryar ya ce burinsu shi ne kame jami'ar da ke garin.

Ya ce; "Mun hade da 'yan uwanmu wadanda suka bullo daga gabas kuma mun shirya cewa in Allah Ya yarda da safe za mu yi yunkurin karbe jami'ar."

Hayaki ya turnike sararin saman garin na Sirte yayin da gidaje da dama ke cin wuta.

Garin na Sirte ne kawai, cikin manya garuruwan da sojojin majalisar rikon kwarya ba ta kwace ba.

Har yanzu dai babu wanda ya san inda tsohon shugaban kasar na Libya, Kanal Gaddafi ya ke.

Kwanaki uku da su ka wuce ya fito da wani sako da aka yadda a gidan talbijin na Syria wanda yake kira ga al'ummar kasar da su yiwa sabuwar gwamnatin kasar bore, saboda a cewarsa ba halatacciyar gwamnati ba ce.