Zaben Shugaban Kasa a Kamaru

A yau ne al'ummomin Jamhuriyar Kamaru ke zaben Shugaban kasa.

'Yan takara ashirin da uku ne zasu fafata, cikinsu har da shugaban kasar mai ci yanzu wato Paul Biya, wanda kuma zai fuskaci wasu manya 'yan adawa irin su Ni John Fru di da Adamou Adam Joya da kuma Garaga Haman Adji.

Shugaba Paul Biya mai shekaru saba'in da takwas a duniya dai ya shafe shekaru ashirin da tara yana mulkin kasar ta Kamaru

Zaben na zuwa ne wasu 'yan makonni bayan da aka mika mulki zuwa wata zababbiyar gwamnati a Zambia cikin ruwan sanyi

Tuni dai hukumar zaben kasar wato Elecam ta ce ta kammala dukkanin shirye shiryen daya kamata na gudanar da zaben.