An yi jana'izar Wangari Maathai

Wangari Maathai Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wangari Maathai

A kasar Kenya, an gudanar da jana'izar girmamawa ta kasa ga matar da ta taba lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya, Wangari Maathai, wadda ta rasu cikin watan jiya a sakamakon cutar sankara.

Wangari Maathai ta yi fice ne a duniya, a sakamakon ayyukanta na kare muhalli, ciki har da kafa wata kungiya ta Green Belt Movement, wadda ta shuka itatuwa miliyan talatin a sassa daban daban na kasar Kenya.

Wannan shi ne karo na uku a tarihin kasar Kenyar da aka taba gudanar da kasaitacciyar jana'izar girmamawa ta kasa.