Nijar za ta gasar cin kofin kwallon kafar Afirka

Tutar Nijar
Image caption Tutar Nijar

A yau wasu kasashen Afrika suka samu gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar da za a yi a badi, a yayinda wasu ta leko ta koma a gare su.

Tawagar Black Stars ta Ghana ta yi katari da sa'a, a yayinda ita kuma ta Super Eagles ta Najeriya ta gamu da rashin sa'a.

Jamhuriyar Nijar dai ta kai labari, domin kuwa kungiyar kwallon kafar kasar ta MENA ta cancanci shiga gasar, duk kuwa da ta sha kashi ne a hannun kasar Masar da ci uku da nema.

Wannan ne karon farko da Nijar din za ta gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirkar.

Jama'a a Nijar su na ta nuna farincikinsu da wannan rawar ganin da 'yan wasan nasu su ka taka.