Mayakan Gaddafi na kara tirjewa a Sirte

Hari a birnin Sirte Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hari a birnin Sirte

Dakarun gwamnatin wucin gadin Libiya sun gamu da jar adawa daga magoya bayan Kanar Gaddafi, yayin da suka kaddamar da wani sabon hari a tsakiyar birnin Sirte, watau mahaifar Kanar Gaddafin, kuma daya daga cikin wuraren da suka rage a hannun magoya bayansa.

A cewar kwamandojin mayakan gwamnatin, sun fuskanci babban kalubale daga masu harbin dauki dai-dai, wadanda suka labe a rufin gidaje, a mummunan yakin da suke gwabzawa akan titunan Sirte din.

Amma kuma in ji shugabannin mayakan, har yanzu suna rike da wuraren da suka kame a jiya.

Likitoci sun ce an kashe mutane akalla goma sha biyu, an kuma raunata wasu fiye da hakan, tun daga lokacin da dakarun dake adawa da Gaddafin suka kaddamar da hare haren a yi-ta-ta-kare a kan Sirte, a ranar Juma'a.