Zaman dar-dar tsakanin Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Sudan

Tutar Sudan Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Sudan ta Kudu da jamhuriyar Sudan na zargin juna da goyawa 'yan tawaye baya

Akwai rashin jituwa tsakanin Sudan da kuma Sudan ta Kudu, amma Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu yace yana da tabbacin cewar za'a iya shawo kan rashin jituwar.

Ya bada misali ne kuma da tattaunawar da aka shafe shekara da shekaru ana yi wacce ta kawo karshen yakin shekaru 21, daga bisani kuma ta haifar da 'yancin kan sudan ta Kudu

Shugaba Kiir da kuma ministocinsa guda takwas suna birnin Khartoum domin tauuatuna wasu batutuwa mahimmai.

Dukkanin bangarorin biyu dai na zargin juna da goyawa 'yan tawaye baya.

Har yanzu dai babu wata yarjejeniya akan nawa sudan ta Kudu zata rinka biya domin tayi amfani da bututu da kuma tashar jiragen ruwan jamhuriyar Sudan domin fitarda mai zuwa kasashen ketare.

Dukkanin bangarorin biyu dai na ikirarin mallakar yankin nan na Abiye, saboda haka ba'a san makomar yankin ba.

Haka kuma ba'a kammala yarjejeniya ba akan iyakokin dake tsakanin kassahen biyu.

Jamhuriyar Sudan da kuma sudan ta kudu sunyi imanin ziyarar shugaba Kiir mahimmin mataki ne na warware sarkakiyar da ake ciki