Shugaban Yemen ya ce zai sauka daga mulki

Ali Abdullah Saleh Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ali Abdullah Saleh

Shugaban kasar Yemen, Ali Abdullah Saleh, ya ce nan da kwanaki masu zuwa zai sauka daga mulki.

A cikin wani jawabinsa a gidan talabijin din kasar, Ali Abdullah Saleh ya ce ba ya kwadayin mulki.

To amma kuma bai fadi ainihin ranar da zai bar mulkin ba.

Ko a lokutan baya ma shugaban ya sha fadin cewa zai sauka daga kan karagar mulkin, yayin da aka kwashe watanni ana zanga zangar neman ya yi murabus.

To amma sai kawai ya sake ra'ayi yayin da aski ya zo gaban goshi.

Tawakul Karman, 'yar fafutukar nan ta kasar Yemen din, wadda a kwanan nan ta sami kyautar Nobel ta zaman lafiya, ta ce 'yan adawa na daukar kalaman shugaba Saleh a matsayin tatsuniya kawai.

To sai dai mukaddashin ministan yada labaran kasar ya shaidawa BBC cewa, a yanzu kam shugaba Ali Abdullah Saleh ya sallama.