An kammala zaben shugaban kasar Kamaru

Shugaba Paul Biya Hakkin mallakar hoto Paul Biya
Image caption Shugaba Paul Biya

A Kamaru an rufe rumfunan zabe, bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a yau.

Shugaban kasar mai ci , Paul Biya, da ya shafe kusan shekaru 30 yana jagorancin kasar, shi ne ya kara da wasu 'yan takarar fiye da 20, ciki har da fitaccen dan adawan nan na jam'iyyar SDF, John Fru Ndi.

Wani wakilin BBC a birnin Douala, cibiyar kasuwancin kasar, ya ce daga farko an fuskanci jinkiri wajen soma zaben, kuma mutane da yawa ba su fito kada kuri'ar ba.

Ya kuma ce, ana sukar lamirin 'yan adawa, kan yadda su ka gaza fitar da wata takamaimiyar manufa, sannan da tsayar da 'yan takara barkatai.

Sai dai 'yan adawar na korafin cewa, baya ga yadda shugaba Biya yayi kane-kane a harkar shirya zaben, rashin kudi, da kuma hana su isasshen lokaci a kafafen yada labarai, yayi masu tarnaki a yakin neman zaben.

Nan da kimanin makonni biyu ne ake shirin bayyana sakamakon zaben.