Gwamnatin rikon Libiya na ikirarin samun galaba a Sirte

Yakin Sirte Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Yakin Sirte

Wasu alamu na nuna cewa, dakarun sabuwar gwamnatin rikon kwaryar Libya, NTC, na dab da kame wani muhimmin yanki na birnin Sirte, inda nan ne mahaifar Kanar Gaddafi. Wasu manema labaru dake wurin sun ce, mayakan na NTC sun shiga ginin wata cibiyar gudanar da taruka, inda a baya mayakan Kanar Gaddafi suka rika nuna tirjiya daga cikinta.

An dai kashe wasu mayakan gwamnatin rikon, an kuma raunata wasu daruruwa, tun daga lokacin da suka kaddamar da hare haren na a yi ta-ta-kare a kan Sirte, shekaranjiya Juma'a.

Ana kuma nuna damuwa game da halin da fararen hular da aka rutsa da su a birnin suke ciki.