Gwamnatin rikon Libiya ta sami galaba a Sirte

Yaki a Sirte Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaki a Sirte

Dakarun sabuwar gwamnati rikon kwaryar Libya ta NTC, sun karbe iko da wani muhimmin yanki na birnin Sirte -- muhimmin gari na karshe dake hannun dakarun dake mara baya ga Kanar Gaddafi.

Manema labaru da ke wurin sun ce, dakarun sun kame wata cibiyar shirya taro, wadda a da mayakan Gaddafi ke rike da ita.

Shugaban majalisar rikon kwaryar, Mustafa Abdul Jalil, ya ce za a 'yantar da kasar baki daya cikin kwanaki masu zuwa.

Garin Bani Walid yanzu haka an masa kofar raggo daga kusurwoyi biyar. Wani wakilin BBC ya ce, ya ga mayakan hukumar ta NTC da dama da aka kashe, da wadanda aka jikkata a wani asibiti.