Danjuma Goje ya kai kan shi hukumar EFCC

A Najeriya, Hukumar da ke yaki da masu yi wa tatttalin arzikin kasar ta'annati, wato EFCC ta tabbatar da cewar tsohon gwamnan jihar Gombe, Senata Danjuma Goje ya shiga hannunta, kuma tana kan yi masa tambayoyi.

Hukumar dai na zarginsa ne da yin sama-da-fadi da kudin jihar da suka kai Naira miliyan dubu hamsin da biyu.

Kazalika kuma, hukumar ta ce tana duba yiwuwar gurfanar da wasu tsofaffin gwamnoni uku da ta kama gaban kuliya, a yau din.

Sai dai wasu kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar na korafin cewa kurari ya fi yawa a cikin aikin hukumar, don haka da wuya wani hukuncin kwarai ya biyo bayan kamun.