An kafa dokar hana yawo a birnin Alkahiran kasar Masar

Zanga zangar Kiristoci a Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu kiristoci a kasar Masar sun yi taho mu gama da jami'an tsaro bayan da suka zargi jami'an tsaron da gazawa wajen kare lafiyarsu

Majalisar zartarwar kasar Masar zata gudanar da wani taron gaggawa don tattauna rikicin daya barke tun bayan da aka hambaradda da shugaba Hosni Mubarak daga karagar mulki a watan Fabrairu. An kashe akalla mutane ashirin da hudu yayin da fiye da mutane dari suka samu raunuka a wani fito na fito da aka yi tsakanin jami'an tsaro da kiristoci mabiya darikar Coptic dake kasar, lamarin da yasa tuni aka sanya dokar hana yawo a tsakiyar birnin Alkahira.

Fira Ministan kasar Essam Sharaf ya fada a wani jawabin da yayi ta gidan talbijin cewa rikicin ya maida kasar baya, inda ya ce wasu makiya na kokarin yin zagon kasa ga dangartakar dake tsakanin sojoji da al'ummomin kasar.

Su dai kiristoci mabiya darikar ta Coptic wadanda ba su wuce kashi goma ba cikin fiye da mutane miliyan tamanin 'yan kasar, sun yi ta sukar hukumomin kasar ne da gazawa wajen karesu daga kai musu hare hare.