Farashin abinci zai ci gaba da tashi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce hauhawar farashin kayayyakin abinci zai ci gaba, lamarin zai kuma haddasa matsalar karancin abinci a kasashen duniya.

A rahotansu na shekara shekara, hukumomin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa kananan kasashen dake dogara kan kayayyakin abincin da ake shigowa da su, su ne suka fi fuskantar hadari.

Sun bayyana cewar, matsalar hauhawar farashin kayayyaki wani babban kalubale ne ga cimma muradin karni na rage mutanan dake fama da yunwa da rabi nan da shekara ta 2015.

Wakilin BBC ya ce ana sa ran matsanancin yanayin da za a shiga shekaru goma masu zuwa zai kara sa farashin kayayyakin abincin hawa, kuma nahiyar Afirka ce lamarin ya fi shafa.