Bam ya hallaka mutane biyu a Maiduguri

Taswirar Arewacin Najeriya Hakkin mallakar hoto System
Image caption Birnin Maiduguri ya yi kaurin suna wajen tashin bama-bamai

A Najeriya, mutane biyu sun rasa rayukansu a sakamakon munanan raunukan da suka samu, bayan da wani bom ya tashi a unguwar Dala da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Mutanen da suka mutun, wadanda suka hada da soja daya da kuma farar hula guda, suna daga cikin mutane 4 da suka ji raunuka a sakamakon tashin bam din.

Rundunar hadin gwuiwar samar da tsaro a jihar, JTF ta tabbatar da afkuwar lamarin, tana mai cewa an kai harin ne kan motar jami'anta.

Sai dai bayanai sun nuna cewa mazauna unguwar da dama sun tsere daga gidajensu sakamakon harbin kan mai tsautsayi da kone-konen shagunan da suka ce jami'an sojin sun yi, bayan tashin bom din.

Ko da a yammacin jiya ma wani bom din ya tashi a unguwar Gwange da ke tsakiyar birnin.