Pedro Pires ya lashe kyautar Mo Ibrahim

Pedro Verona Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pedro Verona shi ne na uku da ya lashe kyautar

Tsohon shugaban kasar Cape Verde Pedro Verona Pires ya lashe kyautar dala miliyan biyar ta Gidauniyar Mo Ibrahim kan kyakkyawan shugabanci a nahiyar Afrika.

Kwamitin bayar da kyautar ya ce Mr Pires, wanda ya sauka daga mulki a watan Agusta, ya taimaka wajen mayar da kasar "wata abar koyi a fannin dimokuradiyya, da zaman lafiya da kuma ci gaba".

An shirya bayar da kyautar ne duk shekara ga shugaban da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya wanda kuma ya bar mulki don kashin kansa.

Sai dai an shafe shekaru biyu ba tare da an samu wanda ya lashe kyautar ba.

Kwamitin ya ce babu wanda ya cancanci samun kyautar.

Kyautar ta dala miliyan biyar, wacce ake bayarwa cikin shekaru 10 ita ce mafi girma a duniya da ake baiwa mutum guda.

Wadanda suka taba lashe gasar abaya sun hada da shugaban Botswana Festus Mogae da na Mozambique Joaquim Chissano.