Babban Bankin Najeriya ya kara kudin ruwa

Gwamnan CBN, Malam Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Gwamnan CBN, Malam Sanusi Lamido Sanusi

Sakamakon halin da tattalin arzikin duniya ke ciki da kuma yadda yake shafar darajar kudin Naira, ya sa Kwamitin dake tsara manufofin kudi a Najeriya kiran wani taron gaggawa yau a Abuja.

A wajen taron, Kwamitin dake karkashin Babban Bankin kasar -CBN ya bayyana daukar wasu matakan riga kafi da suka hada da kara kudin ruwa a bashin da bankunan kasar ke bayarwa da kuma rage yawan kudin dake hannun al'umma.

Haka kuma kwamitin ya dauki matakin nuna goyon baya wajen aiwatar da manufofin da za su bunkasa asusun ajiyar kudaden waje na kasar.

Kwamitin dai ya ce yana ganin wadannan matakai za su hana hauhawar farashin kayyaki tare kuma da kare darajar kudin kasar.