Nijeriya da Nijar zasu karfafa matakan tsaron su

Sojoji a Najeriya
Image caption Najeriya da Nijar zasu hada karfi da karfe wajen karfafa matakan tsaronsu

Supeto janar na 'yan sandan Najeriya Hafiz Ringim ya kammala wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai a Jamhuriyar Niger.

Yayin ziyarar dai ya gana ne da hukumomin 'yan sandan Niger, inda suka cimma wata yarjejeniyar karfafa matakan tsaro tsakanin kasashen biyu, ta hanyar musayar bayanai, bada da horo, da kuma samar da kayayyakin aiki ga jami'an tsaron kasashen biyu.

Najeriya dai na da iyaka mai fadin gaske da Jamhuriyar ta Niger, kuma tabbatar da tsaro akan iyakokin kasashen ya kasance babban kalubale ga kasashen biyu.

Gabannin ziyarar zuwa Jamhuriyar ta Niger din, Supeto janar na 'yan sandan Najeriyar ya yi makamanciyar wannan ziyara a kasashen Ghana da Chadi.

A yanzu haka dai kasashen biyu dake makwabtaka da juna na fuskantar barazanar tsaro.