Isra'ila da Hamas za su yi musayar fursunoni

Gilad Shalit
Image caption Gilad Shalit

Fira ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce an cimma 'yarjejeniya tsakanin Isra'ila da kungiyar Falasdinawa masu fafitika ta Hamas, wadda za ta kai ga sakin sojan nan na Isra'ila da aka Hamass din ta kama, Gilad Shalit.

An dai Saja Gilad Shalit ne a sakamakon wani hari da Hamas din ta kai cikin Isra'ila a shekara ta 2006, kuma tun lokacin batun kama shi ya rika jan hankalin jamaar Isra'ila.

A baya dai, an sha yunkurin ceto shi, amma abun ya ci tura. Sai dai Mr Netanyahu, wanda ke wani jawabi ta gidan talabijin din Isra'ila bayan wani taro na musamman da majalisar ministocinsa ta yi, ya ce Gilad Shalit zai koma Isra'ila a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

A madadin haka, Isra'ila za ta saki kimanin Falasdinawa dubu daya da ta ke tsare da su.