Ana zaben Shugaban Kasa a Liberia

Ana zaben Shugaban Kasa a Liberia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jama'a sun yi layi da suba domin kada kuri'a

Al'umar Liberia sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasar wanda shi ne zabe karo na biyu bayan yakin basasar da kasar ta shafe shekaru 14 ta na fama da shi.

Tunda sanyin safiya ne masu kada kuri'a suka yi dogayen layuka domin sauke nauyin da ke kansu.

Wakilin BBC a Monrovia babban birnin kasar Jonathan Paye-Layleh, ya ce jama'a sun fara hawa layi tunda asuba, duk kuwa da ruwan saman da ake tafkawa a wasu runfunan zaben.

'Yan takarar da ke fafatawa sun hada da shugaba mai ci yanzu Ellen Johnson Sirleaf wacce a makon jiya ne aka bata lambar yabon zaman lafiya ta Nobel.

Tuni dai magoya bayanta ke fatan lambar yabon data samu zai kara mata kwarin guiwa na kaiwa ga zagaye na biyu.

Wakilinmu ya ce Ms Johnson Sirleaf na fuskantar babban kalubale ne daga Winston Tubman, tsohon jakadan kasar a Majalisar dinkin duniya wanda kuma mataimakinsa a takarar wato George Weh shi ne yazo na biyu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2005.

Za a rufe rumfunan zaben ne da misalin karfe shida agogon GMT.

Masu zaben na kuma zabar 'yan majalisar dattawa da na wakilai a zaben.

Liberia ce kasa ta farko da ta fara samun 'yancin kai a Afrika, inda bayin da aka saka daga Amurka suka 'yantar da ita a shekarar 1847.

Shugaban tawagar masu sa ido ta kungiyar Ecowas - shugaban hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Attahiru Jega, ya ce ya na fatan za a gudanar da zaben cikin adalci da kwanciyar hankali.