Yau ake zaben Shugaban Kasa a Liberia

Tutar Kasar Liberia
Image caption A yau al'ummar kasar Liberia zasu gudanar da zaben shugaban kasa

Idan an jima a yau ne za'a fara kada kuri'a a zaben shugaban kasar Liberia wanda shi ne zabe karo na biyu a kasar tun bayan yakin basasar da aka kawo karshensa shekaru takwas da suka gabata.

'Yan takarar da zasu fafata sun hada da shugaba mai ci yanzu Ellen Johnson Sirleaf wacce a makon jiya ne aka bata lambar yabon zaman lafiya ta Nobel.

Tuni dai magoya bayanta ke fatan lambar yabon data samu zai kara mata kwarin guiwa na kaiwa ga zagaye na biyu.

Wakilin BBC ya ce Ms Johnson Sirleaf na fuskantar babban kalubale ne daga Winston Tubman, tsohon jakadan kasar a Majalisar dinkin duniya wanda kuma mataimakinsa a takarar wato George Weh shine yazo na biyu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2005.