Za a fara shari'ar Abdulmutallab gadan-gadan

Umar Faruk Abdulmutallab
Image caption A baya Abdulmutallab ya ce shi zai kare kansa

A ranar Talata ne ake fara shari'ar dan Najeriya Umar Abdulmutallab gadan-gadan - an zarge shi ne da kokarin fasa bam a wani jirgin saman Amurka a shekara ta 2009.

Ana zargin Umar Faruk Abdulmuttalab ne da kokarin hallaka mutane kusan dari ukku wadanda ke cikin jirgin da ke hanyarsa ta zuwa birnin Detroit na Amurka daga birnin Amsterdam.

Umar Faruk Abdulmuttalab ya musanta wannan zargi, inda ya dage akan zai kare kansa, ko da ya ke daga bisani ya amince wani Lauya ya wakilce shi.

Editan BBC Mansur Liman, ya ce wannan dai wata shari'a ce da za ta ja hankalin jama'a da dama, ba wai kawai a Amurka ko Najeriya ba, a'a har ma da sauran sassa na duniya.

Musamman ganin yadda ta zo 'yan kwanaki kalilan da hallaka Anwar Al-Awlaqi, wani jagoran kungiyar Al-ka'ida a kasar Yemen, wanda hukumomin leken asiri na Amurka suka dade suna dangantashi da Umar Faruk Abdulmuttalab.

Za'a fara wannan shari'a ce da jin bayanan share fage daga dukkkanin bangarorin.

Tun farko dai Umar Faruk Abdulmuttalab ya tsaya kai da fatan akan cewar shi ne zai gabatar da wannan bayani da kansa, a madadin Lauyan da aka wakilta masa.

To amma ranar Juma'ar da ta gabata, Umar Abdulmuttalab ya amince Lauya Anthony Chambers, ya gabatar da wannan bayanin share fage a madadinsa.

Gabatar da shaida

Tun farko dai sai da aka kwashe kwanaki ukku a makon jiya gabanin a kammala zabar mutanen da za su taimakawa alkali yanke hukunci.

A lokacin da aka ce Umar Abdulmuttalab ya yi ta yin wasu kalamai a cikin kotun da suka hada da cewar, '''Masu Kishin Islama za su gama da wanann cutar daaji da ake kira Amurka.''

Ana dai sa ran Umar Faruk Abdulmuttalab zai nemi wani pasinja, mai suna Kurt Haskell daya daga cikin pasinjojin jirgin da aka yi zargin ya nemi ya tarwatsa domin bayyana a gaban kotun ya bada shaida.

Haskell mutum ne da ya wallafa a dandalinsa na shafin internet cewar an baiwa Umar Faruk Abdulmuttalab wani bomb na bogi ne -- domin a tsara wani shiri na kai harin ta'addanci, yadda Amurka za ta kafa hujja akan irin makudan kudaden da ta ke kashewa a yanki da ta'addanci da jama'a ke ci gaba da dawowa daga rakiyarsa.

Rahotanni dai sun ce yunkurin tarwatsa jirgin samar ya ci tura ne, a yayin da bamb din da aka dinke a kamfen Umar Faruk Abdulmuttalab ya ki tashi, sai dai wata 'yar wuta ta tashi, inda kuma pasinjojin da kuma ma'aikatan jirgin suka samu suka ci karfinsa.

Umar Faruk Abdulmuttalab, dan shekaru 24 da haihuwa dai, da ne ga wani fitaccen hamshakin attajiri a Najeriya, ya kuma yi karatunsa a wuraren da suka hada da Najeriya da Togo da Ingila, inda daga bisani aka ce ya ziyarci kasar Yemen.

Karin bayani