Za'a fusknaci karancin wuta a Najeriya

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Za'a fuskanci karancin wuta a Najeriya a 'yan kwanakin nan

A Najeriya, daga a yau Talata ne kamfanin samar da wutar lantarki na kasar wato PHCN, zai rufe wasu tashoshinsa na samar da hasken wutar lantarki masu amfani da iskar gas guda biyar domin gudanar da wadansu gyare-gyare.

Hakan dai a cewar kamfanin zai haifar da raguwar adadin wutar da ake samu da megawatt 1,415.

Sai dai kamfanin ya ce zai yi iyakacin kokarinsa domin takaita asarar da hakan zai haifar ga 'yan kasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin da ma mahukuntan kasar ke bugar kirjin cewa an fara samun ci gaba a fannin samar da wutar lantarkin.

Batun samar da hasken wutar lantarki mai dorewa dai wani babban kalubale ne ga Najeriya

Masu lura da al'amura dai na ganin cewar yanayin da za'a shiga yanzu zai sake sanya 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali musamman masu amfani da hasken wutar wajen gudanar da sana'oi