An daure tsohuwar Fira ministar Ukraine

Yulia Tymoshenko Hakkin mallakar hoto none
Image caption Tymoshenko na zaune a kotu tare da mijinta da kuma 'yarta

An yankewa tsohuwar Fira ministar Ukraine Yulia Tymoshenko hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, bayan da aka same ta da laifin saba wa dokar aiki.

Alkalin ya ce ta wuce gona-da-iri lokacin da sanya hannu kan wata yarjejeniyar iskar gas da kasar Rasha a shekara ta 2009.

Mrs Tymoshenko ta ce tuhumar da ake mata na da alaka da siyasa, sannan ta yi alkawarin ci gaba da fafutikar dimokuradiyya a Ukraine "har karshen rayuwarta."

An jibge 'yan sandan kwantar da tarzoma a wajen kotun inda magoya baya da masu adawa da ita suka taru, kuma an samu 'yar tarzoma a wajen.

Alkalin ya kuma nemi tsohuwar Fira Ministan da ta biya dala miliyan 186 na asarar da kamfanin gas na kasar ya yi sakamakon yarjejeniyar.

A lokacin da ake karanta hukuncin, Mrs Tymoshenko ta rinka katse alkalin, tana cewa "zan yi iya kokarina wajen kare sunana", ta kara da cewa Ukraine ta koma tafarkin kama-karya na shekarun 1937 - lokacin mulkin Tarayyar Soviet.

Amurka da Tarayyar Turai sun yi Allah wadai da tuhumar tata da kuma wasu na kusa da ita, suna cewa yunkuri ne na takurawa 'yan adawa.

Jami'an Turai sun ce daure Mrs Tymoshenko ka iya zama wani babban cikas ga yunkurin kasar na hadewa da Tarayyar Turai.