An tuhumi wasu mutane biyu a Amirka

Antoni Janar na Amurka, Eric Holder Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Antoni Janar na Amurka, Eric Holder

Mahukuntan Amurka sun ce sun tuhumi wasu 'yan kasar Iran biyu kan shirin kashe jakadan kasar Saudiyya a Washington.

Antoni janar na Amurka, Eric Holder ya ce kasar Iran ce ta kitsa kai shirin tare da daukar nauyinsa, kuma za'a dorawa Tehran alhakin abin da ya faru.

Mr Holder ya ce an tuhumi mutanen biyu a New York da hada baki a yi kisa da yin amfani da makaman kare dangi da kuma aikata ta'addanci.

Daraktan hukumar yaki da manyan laifuka ta Amurka FBI, Robert Mueller ya ce ba karamin asarar rayuka harin zai janyo ba, da an yi nasarar kai shi.