Annobar kwalara a yammaci da tsakiyar Afirka

Masu fama da kwalara
Image caption Masu fama da kwalara

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya, UNICEF, yayi kiran da a kara tashi tsaye wajen yaki da abinda ya bayyana da: daya daga cikin annobai mafi muni na kwalara da nahiyar Afirka ta fuskanta.

A cikin rahoton da hukumomi lafiya na majalisar dinkin duniya suka fitar, sun ce a Najeriya da kuma wasu kasashen Afrika hudu ne ake samun kashi 90 cikin dari na mace-mace, sanadiyyar kwalara.

Rahoton ya ce a wannan shekarar kawai, annobar ta kwalara da ke bazuwa yankunan yammaci da tsakiyar Afrika, ta kama sama da mutane dubu 85, kuma ta hallaka kusan dubu biyu da rabi kawo yanzu.

Asusun na UNICEF ya nuna fargaba musamman game da bazuwar cutar zuwa Kinshasa, babban birnin jamhuriyar demokradiyyar Congo.