Umar Faruk Abdulmutallab ya amsa laifinsa

Umar Faruk Abdulmutallab
Image caption A baya Abdulmutallab ya ce shi zai kare kansa

Dan Najeriyar da ake zargi da yunkurin kai hari a wani jirgin saman Amurka a shekarar 2009 Umar Faruk Abdulmutallab, ya amince cewa ya yi niyyar aikata abinda ake zarginsa da shi. A yanzu haka ana ci gaba shari'ar a birnin Detroit na Amurka.

Ana zargin Umar Faruk Abdulmuttalab ne da kokarin hallaka mutane kusan dari ukku wadanda ke cikin jirgin da ke hanyarsa ta zuwa birnin Detroit na Amurka daga birnin Amsterdam.

A baya Umar Faruk Abdulmuttalab ya musanta wannan zargi, inda ya dage akan zai kare kansa, ko da ya ke daga bisani ya amince wani Lauya ya wakilce shi.

Editan BBC Mansur Liman, ya ce wannan dai wata shari'a ce da za ta ja hankalin jama'a da dama, ba wai kawai a Amurka ko Najeriya ba, a'a har ma da sauran sassa na duniya.

Musamman ganin yadda ta zo 'yan kwanaki kalilan da hallaka Anwar Al-Awlaqi, wani jagoran kungiyar Al-ka'ida a kasar Yemen, wanda hukumomin leken asiri na Amurka suka dade suna dangantashi da Umar Faruk Abdulmuttalab.

A ranar Talata ne aka fara shari'ar gadan-gadan da jin bayanan share fage daga dukkkanin bangarorin.

Tun farko dai Umar Faruk Abdulmuttalab ya tsaya kai da fatan akan cewar shi ne zai gabatar da wannan bayani da kansa, a madadin Lauyan da aka wakilta masa.

To amma ranar Juma'ar da ta gabata, Umar Abdulmuttalab ya amince Lauya Anthony Chambers, ya gabatar da wannan bayanin share fage a madadinsa.

Rahotanni dai sun ce yunkurin tarwatsa jirgin samar ya ci tura ne, a yayin da bamb din da aka dinke a kamfen Umar Faruk Abdulmuttalab ya ki tashi, sai dai wata 'yar wuta ta tashi, inda kuma pasinjojin da kuma ma'aikatan jirgin suka samu suka ci karfinsa.

Umar Faruk Abdulmuttalab, dan shekaru 24 da haihuwa dai, da ne ga wani fitaccen hamshakin attajiri a Najeriya, ya kuma yi karatunsa a wuraren da suka hada da Najeriya da Togo da Ingila, inda daga bisani aka ce ya ziyarci kasar Yemen.

Karin bayani