Harin ramuwar gayya na so kaiwa —Umar Mutallab

Umar Farouk Abdulmutallab
Image caption Umar Farouk Abdulmutallab

Matashin nan dan Najeriya, Umar Faruk Abdulmutallab da ake zargin cewa ya yi yunkurin tarwatsa wani jirgin sama a birnin Detroit na kasar Amurka a ranar Kirsimatin shekara ta 2009, ya ce ya amince da aikata laifin.

A rana ta biyu ta zaman kotun, ya shaida mata cewa yunkurin da ya yi na ta da wani bom kokari ne na sauke wani nauyi.

Wakilin BBC ya ce a wani jawabin da ya gabatar wa kotun ya ce addininsa ya dora masa hakkin yin ramuwar-gayya ga abin da ya bayyana da hare-haren da Amurka ke kai wa musulmi.

A yanzu dai, Umar Faruk Abdulmutallab na fuskantar hukuncin daurin-rai-da-rai bisa tuhumce-tuhumcen da ake masa guda takwas, ciki har da yunkurin kisan kusan mutum dari uku, wadanda ke cikin jirgin saman, a lokacin da yake yunkurin ta da wani bom din ya boye cikin kamfensa.

Umar Faruk a cikin nutsuwa ya fara amsa tambayoyi daga alkalin kotun mai shari'a Nancy Edmuns, kafin daga bisani ya amsa cewa ya aikata laifuka takwas din da ake tuhumarsa da su, wadanda suka hadar da hadin baki don aikata ta'addanci, da kuma yunkurin amfani da makamin kare dangi.

Zargin Amurka

Daga bisani ya ce bom din da aka sanya cikin kamfansa da ya yi yunkurin tarwatsa jirgin da shi, wani makami ne mai albarka, da ya yi yunkurin ceto rayukan Musulmin da ba su ji ba basu gani ba da shi.

A cikin wani jawabi na mintina shida da ya yi, Umar Faruk ya hakikance cewa, matakin da ya dauka daidai yake, kuma aininhin laifi na ga manufofin harkokin wajen Amurka.

"Ni mai laifi ne a kan wannan tuhumar karkashin dokokin Amurka, amma ba karkashin tanade-tanaden alkur'ani ba.

"Ya kamata a gargadi Amurka da cewa, idan ta ci gaba da dagewa da kuma yaba wa yin batanci ga Annabi Muhammadu, ta kuma ci gaba da kashewa da kuma marawa wadanda suke kashe musulmi, to Amurka ta jira wani babban bala'i daga hannun Mujahidai." In ji Umar Faruk

Ya kuma kara da cewa, ya amince ya kai harin ne domin ya mayar da martani ga mara bayan da Amurka ke yi wa kasar Israela da kuma daukar fansar kashe Musulmin da basu ji ba basu gani ba a Palasdinu, da Yemen, da Iraqi, da Somalia, da Afghanistan da sauransu.

Abdul Mutallab ya kuma ce, idan kuka yi mana dariya a yanzu, to mu ma za mu yi muku dariya a ranar tashin alkiyama.

Yanke shawarar amsa laifi

Lauyan da kotu ta nada wa Abdulmutallab Anthony Chambers, ya ce mutmin da yake karewa, ya yanke shawarar amsa laifin ne, sabanin shawarar da ya bashi:

"Abdulmutallab ya yanke shawara, kuma shawarar da ya yanke ita ce ta amsa laifi. Wannan mataki ne da ya sabawa shawarar da lauya ya bashi. Mataki ne da ya zabi ya dauka, kuma yana ganin shi ne dai-dai. Mun so mu ci gaba da shari'ar, amma kuma mun amince da shawarar da ya yanke." In ji Anthony Chambers.

Shi dai yunkurin harin na watan Disambar shekarar 2009 wanda bai yi nasara ba, ya gaza ne saboda kayan fashewar da aka yi amfani da su ba su tarwatse ba gabadaya, sai dai sun haifar da wuta, abinda ya sa fasinjoji a cikin jirgin suka rirrike shi suka kashe wutar.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Umar faruk Abdul Mutallab na dauke da hukuncin daurin akalla shekaru talatin ba tare da afuwa ba, kuma dole a yi zaman jarum din a jere, hakan na nufin ana iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai har iya karshen rayuwarsa.

Za a yanke wa Abdul Mutallab hukunci ne a ranar sha biyu ga watan Janairun shekara mai zuwa.