Ana zargin gwamnatin Goodluck da son kai wajen ayyukan raya kasa

Shugaba Goodluck Ebele Jonathan na Najeriya
Image caption Alkaluma sun nuna cewa sama da kashi tamanin bisa dari na irin kwagilolin da gwamnatin Najeriya ta bayar, ana yin su ne a yankin Niger-Delta.

A Najeriya wasu 'yan kasar na kokawa dangane da abinda suka ce son rai da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya ke nunawa wajen aiwatar da ayyukan raya kasa da kuma nade-naden mukamai.

Masu koken wadanda suka fito daga arewacin kasar na zargin cewa gwamnatin Najeriya ta fi fifita yankin kudancin kasar.

Wasu alkaluma da Hukumar da ke tantance kwangilolin gwamnati ta fitar sun nuna cewa daga rantsar da shugaban Najeriyar zuwa yanzu, sama da kashi tamanin bisa dari na kwagilolin da gwamnatin ta bayar, ana yin su ne a yankin Niger-Delta, yankin da shugaban kasar ya fito

Sai dai gwamnatin Kasar ta musanta zargin, tana mai cewa mafi yawan ayyukan an faro su ne tun zamanin marigayi shugaba Umaru Musa `Yaradua.