Kotu ta yanzke hukunci kan karar zaben gwamnan Kaduna

A Najeriya, kotun sauraron kararraki a Kaduna, ta yi watsi da wani koken da jam'iyyar CPC ta kai ma ta, inda take kalubalantar zaben mista Patrick Ibrahim Yakowa a matsayin gwamnan jahar.

A cewar jam'iyyar ta CPC, a lokacin zaben na watan Afrilu, an yi aringizon kuri'u, da amfani da karfin gwamnati, da kuma sauran hanyoyin magudi, domin ganin mista Patrick Ibrahim Yakowan ya yi nasara.

Alkalan kotun na yau sun ce, jam'iyyar CPCn ta kasa gabatar da kwararan shaidu, dangane da zarge-zargen da ta yi.

Amma da alamun akwai sauran rina a kaba, domin kuwa CPCn ta ce za ta daukaka kara.