'Yan bindiga sun kama wasu ma'aikatan agaji a Somalia

Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab

Wasu 'yan bindiga sun kama mutane biyu ma'aikatan agaji a babban sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab a Somalia.

Wani kakakin 'yan sanda ya ce an kama mutane biyu ne 'yan asalin kasar Spain, wadanda ke ma kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontieres aiki.

Kungiyar agajin ta ce an kashe direbansu dan kasar Kenya har lahira.

A sansanin na Dadaab akwai dubun-dubatar 'yan Somaliar da suka tsero daga yankunan kasarsu da ake fama da yunwa. Da ma dai akwai matukar rashin kwanciyar hankali a yankin na kan iyaka.

Kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ba abin amincewa ba ne a ce mutane da ke kokarin ceton rayuka an kai masu wannan irin mummunan hari.