Mun fara shawo kan matsalar Blackberry - RIM

Wayar Blackberry Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption RIM ya alakanta matsalar da lalacewar na'ura

Kamfanin RIM da ke samar da wayar salula ta Blackberry ya ce al'amura "sun fara daidaita" bayan da masu amfani da wayar suka shafe kwana uku suna fuskantar matsala.

Miliyoyin masu amfani da wayar ne suka samu cikas wajen aika sakonnin text da kuma na email, inda mafi yawansu suka rinka bayyana takaicinsu ta hanyar sada zumunta ta Twitter.

RIM ya alakanta matsalar da lalacewar wata babbar na'urarsa.

Masu amfani da wayar sun fara fuskantar matsalar ne tun ranar 10 ga watan Oktoba, kafin lamari ya ci gaba da yaduwa a sauran sassan duniya.

A ranar Alhamis kamfanin RIM ya fitar da sanarwa, inda ya ce al'amura "sun fara daidaita" a nahiyar Turai da yankin gabas ta tsakiya da Afrika da kuma India.

"Za mu ci gaba da sa ido dare da rana domin ganin al'amura sun ci gaba da daidaita," karin bayanin da aka wallafa a shafinsa na intanet.

Suma a nasu bangaren kamfanonin layukan waya na ci gaba da turawa masu mu'amala da su sakon bada hakuri kan matasalar da aka fuskanta.

Alal misali a Hadaddidiyar Daular Larabawa, manyan kamfanonin layukan waya biyu na kasar sun ce za su bawa masu amfani da wayar ta BB kwanaki uku da za su ci moriyar shiga kafar Internet kyauta, a matsayin tausa kirji na matsalar da aka fuskanta.

Kimanin Mutane Miliyan 70 ne aka kiyasta cewa suna amfani da wayar ta BB a duniya, inda wayar ke gogayya da takwararta ta I Phone da kamfanin Apple ke kerawa.