Standard and Poors ta rage darajar Spain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cibiyar Standard and Poors na auna karfin kasashen wajen biyan basusukan da ke kansu.

Cibiyar Standard and Poors mai auna mizanin basusukan kasashe ta rage darajar kasar Spain a wajen biyan basussukan da ke kanta.

Wannan ya biyo bayan irin matsalar tattalin arzikin kasashen Turai da ke amfani da kudin Euro su ka shiga.

Matakin da cibiyar Standard and Poors ta dauka na rage darajar Spain na sauke nauyin basusukan da ke kanta ya biyo bayan da wanda cibiyar Fitch ta yi.

Wannan dai ya yi nuni da irin fargabar da aka shiga a yayinda tattalin arzikin kasar ke ci gaba da durkushewa.

Abun da aka fi maida hankali a kai shine yadda rashin aikin yi ya karu wanda kuma ya jefa tattalin arzikin kasar cikin wani yanayi na rashin tabbas.

Basusukan da kasar ta karba na dada karuwa ne musamman ma a hannun 'yan kasuwa a kasar.

Cibiyar Standard and Poors ta yi gargadin cewa tabarbarewa tattalin arzikin abokan huldan Spain na iya zama da babban illa ga kasar, a yayinda kuma bankunan kasar za su