An zargi 'yan sanda da cin zarafin jama'a a Sudan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yankin Kordofan na kan iyakar Sudan ne da Sudan ta kudu

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama dake Amurka ta ce ta samu sabbin shaidu da ke nuni da cewa 'yan sandan kasar Sudan sun ci zarafin fararen hula a yankin kudancin Kordofan a farkon wannan shekaran a bainar Sojojin kiyayye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar.

Kungiyar mai suna 'Enough project' wadda ke sa ido kan rikicin Sudan ta ce mutane da dama ne su ka shaida yadda 'yan sandan kasar Sudan ke kashe da kuma satar fararen hula a kusa da sansanin Sojojin kiyayye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kusa da garin Kadugli.

Kungiyar dai ta buga hotunan da aka dauka da tauraron dan adam wanda ke nuni da yadda 'yan sanda suka cika yankin.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi kira da aka gudanar da bincike mai zaman kansa.

An dai samu barkewar tashin hankali ne a kudancin Kordofan a lokacin da makwabciyar ta Sudan ta kudu ta samu 'yancin kai.

Jonathan Hutson, direktan yadda labarai na kungiyar The Enough Project wadda ke sa ido a rikicin Sudan ya shaidawa BBC cewa wadanda su ka gani da ido sun shaidawa kungiyar cewa 'yan sanda na da hannun wajen kashe da kuma satar mutane a garin kadugli.

"Kusan a kullum 'yan sanda a yankin na satar mutanen da basu da gidaje wanda kuma ke karkashin kulawar sojojin kiyayye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a wani sansani na Majalisar Dinkin Duniya dake Kadugli." In ji Jonathan Hutson.

Mista Huston ya ce sun tsare mutane a wasu lokutan, kuma sun kashe wasu a daidai kusa da sansanin Majalisar Dinkin Duniya a yayinda sojojin kiyayen zaman lafiya na kasar Masar su ka zura musu ido.

Kasar Sudan dai ta karyata rahoton kungiyar inda ta ce bashi da tushe.