BBC ta yi Allah wadai da hukunci kan Usmonov

Urunboy Usmonov
Image caption BBC ta amince cewa Urunboy Usmonov ba shi da wani laifi

Kafar BBC mai yada labarai zuwa kasashen waje ta yi Allah wadai da laifin da aka ce an samu wakilinta a kasar Tajikistan, Urunboy Usmonov.

A ranar Juma'a ne mahukunta a kasar Tajikistan suka samu Urunboy Usmonov da laifin kasancewa dan wata kungiyar masu kishin Islama da aka haramta - kuma aka yanke masa hukuncin shekaru uku - sai dai an yi masa afuwa.

"Mr Usmonov da BBC sun sha musanta zargin, kuma Mr Usmonov ba shi da wani laifi," a cewar wata sanarwa da BBC ta fitar.

"BBC ta yi imanin cewa babu wani laifi da aka same shi da shi, kuma za a amince ne kawai idan an wanke shi kwata-kwata."

Duk da an yi masa afuwa, Mr Usmonov ya yi niyyar daukaka kara domin wanke kansa.

A cewar Peter Horrocks, Daraktan sashin BBC da ke watsa shirye-shirye zuwa kasashen duniya, "Za mu ci gaba da tallafawa Urunboy kuma muna fatan daukaka karar zai dawo masa da kimarsa ta gogaggen dan jarida kuma marubuci.

"Za kuma mu ci gaba da neman bayani kan cin zarafi da azabtarwar da Urunboy ya fuskanta a lokacin da ya ke tsare."

A lokacin shari'ar Mr Usmonov, ya shaida wa kotun cewa an azabtar da shi lokacin da aka kamashi daga ranar 13 ga watan Yunin bana, inda jami'an tsaro suka rinka kona masa hannu da taba-sigari.

Ya kuma ce an tilasta masa amince wa da wasu bayanai da aka rubuta masa.