Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Illolin cutar Numonia ga yara

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Wannan cuta na yin illa matuka ga yara

Cutar Numonia kwayar cuta ce da idan mutum ya kamu da ita, kan janyo kumburin wani bangare na huhu, wanda kan sa wurin da ya kumbura ya cika da ruwa, ta yadda numfashi zai yi wuya.

Sashen lafiya na BBC ya yi karin bayani da cewa idan cutar Numonia ta shiga jikin dan adam, tana addabar numfashi ne, ta hanyar kawo tarnaki a musayar iskar tsakanin wadda mutum ke shaka da kuma wadda yake fitarwa.

Daga cikin alamomin cutar da sashen lafiya na BBC ya bayyana, duk da dai cewa cutar ta danganta da musabbabin da ya janyota, sun hada da zazzabi mai zafi, da yawan gumi, da numfashi sama sama, da ciwon kirji musamman a lokacin da wanda ya kamu da ciwon ke tari ko kuma in ya ja dogon numfashi.

Sauran alamomi sun hada da koren kaki da jini a ciki, da ciwon kai da na gabobi, da tashin zuciya da hararwa, har ma da gudawa.

Duk da dai cewa kowa na iya kamuwa da cutar Numonia, amma Hukumar Lafiya ta duniya WHO tace ta fi yin tsanani a jikin yara, inda tace ita ce babbar cuta daya da tafi yawan salwantar da rayukan yara.

A wani bincike da hukumar WHO tare da hadin gwuiwar asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da kuma gidauniyar Bill & Melinda Gates, suka yi, na nuni da cewa a duk shekara, fiye da yara miliyan 150 ne ke gamuwa da cutar Numonia a duniya.

Kuma fiye da rabin wannan adadin, na faruwa a kasashe goma sha biyar da suka hada da India da Najeriya, da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Pakistan da kuma Afghanistan a can sama.

Binciken ya kara da cewa a shekarar 2008 kadai, kashi daya bisa hudu na yaran da suka rasu a duniya, wato kwatankwacin yara miliyan biyu kenan, sun rasu ne sakamakon cutar Numonia.

Saboda girman wannan matsala ya sa a shekarar 2009 manyan hukumomin lafiya na duniya kamar su WHO da Unicef suka kaddamar da wani gangami na yaki da cutar a duk fadin duniya.

A bana, an kaddamar da rigakafin cutar Numonia a Sansanin 'yan Gudun Hijira na Dadaab dake kasar Kenya, domin magance cutar a tsakanin yaran da ke neman mafaka a can.