An zargi Bishop da rufa-rufa wajen yadda hotunan batsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An zargi mujami'ar da yin rufa rufa kan wani limamin coci

A karon farko an tuhumi wani Bishop din darikar Roman Katolika a Amurka da babban laifi yin rufa-rufa kan batun cin zarafin wasu yara a yankin da yake iko da shi.

An zargi Bishop Robert Finn na yakin birnin Kansas a Jihar Missouri da kin kai karar wani limamin coci da aka samu da hotunan batsa na yara a kumfutar sa.

An dai kuma zargin cocin ne da lallata shaidun da ake da su akan malamin cocin.

Sai dai Bishop din bai amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

Masu shigar da kara dai sun yi nuni da yadda shugabannin cocin su ka yi kokarin boye batun domin kada jama'a da kuma 'yan sanda su sani.

A watan Mayun shekarar da ta gabata, an gargadi Cocin kan halayen Reverend Shawn Ratigan, inda shugaban wata Makaranta inda ya ke koyarwa ya ce malamin na bayyana dabi'ar da bata dace ba idan yana tare da yara.

A watan Disamban shekarar da ta gabata ne wani mai gyaran kumfuta ya ga hotunan batsa na yara da shekarun su basu wuce biyu ba a kamfutar malamin cocin, kuma yawancinsu mata ne.

Father Ratigan ne dai ya dauki wasu daga cikin hotunan da kan shi.

An dai fadawa Bishop Robert Finn batun, amma sai ya ki ya shaidawa 'yan sanda abun da ke faruwa.

Masu shigar da kara sun ce Bishop din tare da wasu manyan malaman cocin sun yi kokarin boye batun sannan kuma su ka lallata shaidar da ake da su a kan malamin cocin a yayinda su ka mayarwa iyalinsa kumfutar.

An dai tseguntawa 'yan sanda abun da ke faruwa ne a watan Mayun wanan shekara.

Bishop Finn da kuma cocin na yankin birnin Kansas na fuskantar tuhumar taimakawa wajen yadda hotunan batsa na yara, kuma wannan shine tuhumar aikata babban laifi da aka taba yiwa wani Bishop din darikar Roman Katolika a Amurka.

Wadanda ake zargi dai basu amsa laifi ba, amma Bishop din dai ya nemi ahuwa game yadda ya tafiyar da al'amura.