Za'a fara binciken rikicin kasar Ivory Coast

Image caption Luis Moreno-Ocampo

Babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Luis Moreno-Ocampo, ya isa kasar Ivory Coast a wani bangari na binciken da ake yi a kan rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa.

Luis Moreno-Ocampo zai gana da wadanda rikicin ya rutsa da su da kuma wakilan gwamnati da na 'yan tawaye.

Ana dai zargin dakarun da ke biyayya ga shugaban kasar mai ci, Alassane Ouattara da abokin hamayyarsa, Laurent Gbagbo, da cin zarafin al'umma a watanni biyar din da aka kwashe ana gwabza fada.

Ana dai ganin rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane dubu uku.

Mista Ouattara ne dai ya bukaci kotun duniyar ta gudanar da bincike bayan ya hau kan karagar mulki a watan Mayu.