An sabunta: 15 ga Oktoba, 2011 - An wallafa a 06:05 GMT

Za'a koya wa dalibai darasin zaman lafiya a Filato

Jihar Filato dai ta dade tana fama da rikicin addini da na siyasa

Hukumomi a jihar Filato da ke arewacin Najeriya sun bayyana cewa za su sanya darasin zaman lafiya a cikin darussan da ake koyarwa a makarantun firamare da sakandaren jihar.

Wannan ya biyo sakamakon tashe-tashen hankulan da jihar ke yawan fuskanta wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Rikicin dai ya haifar da zaman-doya-da-manja tsakanin musulmi da kirista.

Wannan kuwa ya biyo bayan wani littafi ne da wata kungiyar kare hakkin bil-Adama mai suna Civil Rights Congress ta wallafa domin rarrabawa ga makarantu a fadin jihar ta Filato, matakin da gwamnatin jihar ta ce ta yi marhabun da shi domin ya yi dai dai da tsare-tsaren magance matsalar tashe-tashen hankulan jihar.

To sai dai kuma hukumomin jihar ta Filato sun tabbatar da cewa akwai kalubale wajen koyar da dalibai darasin zaman lafiyar, domin su kansu malamai a jihar na bukatar a ilmantar da su kafin fara koyar da wannan darasi.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.