Hammond ne sabon sakataren tsaron Burtaniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakataren harkokin tsaron Burtaniya, Philip Hammond

Sabon sakataren tsaron Burtaniya Philip Hammond ya sha alwashin inganta harkakin tsaron kasar a yayinda ya kama aiki bayan da ya maye gurbin Liam Fox wanda ya yi murabus a ranar Juma'a.

Tsohon sakataren tsaro, Liam Fox ya ajiye aikin ne dai bayan an yi kwanaki ana ce-ce-ku-ce a kan dangantakarsa da abokinsa, Adam Werrity.

Mista Fox na tafiya da Werrity ne wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

Dokta Fox dai ya kasa ba da bayani a kan dalilan da suka sa abokin nasa, wanda bai rike da wani mukami a hukumance, ke halartar tarukan ma'aikatar tsaro, ya kuma yi tafiye-tafiye tare da shi zuwa kasashen waje.

BBC ta samu bayanin cewa wani bincike a karkashin jagorancin shugaban ma'aikatan Birtnaiya zai yi kakkausar suka a kan abubuwan da Mista Fox ya aikata.

Jam'iyyar adawa ta Labour ta yi kira a kara sa ido sosai a kan ministoci da masu ba su shawara, bayanda Skataren Tsaro Liam Fox yayi murabus.

Sabon Sakataren harkokin tsaron Philip Hammond dai ya ce zai aiwatar da shirye shirye masu inganci da za su habbaka harkokin tsaron a Burtaniya.

Ya ce har wa yau, sai tabbatar da cewa a samu isasun kudaden gudanarwa a ma'aikatar tsaron kasar.

Mista Hammond dai ya yaba da ayyukan da Mista Fox ya yi inda ya ce zai dora akai.

Mista Philip Hammond ya shiga majalisa ne tun a shekarar 1997 a karkashin inuwar jam'iyyar Conservative.