Ministocin G20 sun kammala taro kan matsalar tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ministocin kudi na kasashe ashirin masu ci gaban tattalin arziki, wato G20, sun kammala taro a kan matsalar bashin da ta addabi kasashen da ke amfani da kudin euro.

Ministocin dai sun ce cewa sun yi amanna shugabannin kasashen Turai na samun ci gaba a kokarin magance matsalar.

Ministan Kudin Birtaniya, George Osborne ya ce tattaunawar ta yi armashi

Shi ko Ministan Kudin Amurka, Timothy Geithner cewa ya yi ya ji abubuwa masu karfafa gwiwa dangane da wani sabon shiri kan yadda za a shawo kan matsalar ko da yake bai sami cikakken bayani ba.

Ministan kudi na Faransa, Francois Baroin, ya jaddada cewa sai a karshen mako mai zuwa za a yi cikakken bayani, a lokacin taron shugabannin Tarayyar Turai a Brussels.