'An yi kuskuren shigar da Girka cikin Euro' in ji Sarkozy

Nicolas Sarkozy Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nicolas Sarkozy

Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, ya ce kuskure akayi da aka amince da Girka ta shiga kungiyar Tarayyar Turai a shekara ta 2001. A wata hira da yayi da gidan talabijin na Faransa, Sarkozy ya ce bai kamata a shigar da Girka cikin kungiyar ba saboda abunda ya kira: karairayin da ke cike da alkalumman tattalin arzikin ta.

Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan shugabannin kasashen turai sun cimma yarjajeniyar magance matsalar bashi a nahiyar ta turai.

A murtanin da ya mayar, ministan harkokin wajen Girka, Stavros Lambrinidis, ya ce ba kasarsa ce tushen matsalar kudaden da kasashen yankin Euro ke fuskanta ba.