Isra'ila ta wallafa sunayen fursunonin da za a yi musaya

Image caption Kusan fursononi dubu daya ne ake kyautata zaton za'a yi musaya da su.

Isra'ila ta wallafa sunayen fursunoni Falasdinawa kusan dari biyar da za ta yi musaya da su da wani sojin ta da aka kama Gilad Shalite.

Masu gwagwarmayar Falasdinu ne dai su ka kama shi tun a shekara ta dubu biyu da shida.

Shugaban Isra'ila Shimon Peres na tare da takardun kusan fursunonin dari biyar a gabansan, amma ya ce ba zai yi musu ahuwa a hukumance ba, sai Isra'ila ta samu damar daukaka kara a kan batun.

Wasu daga cikin fursunonin da za'a saki dai sun hada da wadanda aka yi musu daurin rai da darai saboda an same su da laifin harbi ko kuma shirya kunar bakin wake.

Amma akwai yiwuwar babban kotun Israila ba za ta hana yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta cimma da masu fafutukar Falasdinu ba, wanda kuma ya samu goyon bayan mutane da dama a kasar.

Ana kyautata zaton za'a fara sakin Falasdinawa ne a ranar Talata, sannan kuma sai a saki Gilad Shalit shima.

Za'a saki sauran Falasdinawan ne su kusan dari biyar a tsawon watanni biyu.